Frequently Asked Questions Hausa

FAQ is available in English, Yoruba, Egun, Ibo and Hausa. Click the laguage button to select your choice.


 • MENENE HOMS DIN LEGAS?

  +

  Shirin Samun Mallakin Gida na Legas wato (Lagos HOMS) shine makunshin kyauta wanda zai bada dama masu zaman a jihar Legas su samu mallakin gida na kansu. HOMS na Legas za ta bada shirin aro na gida wanda bai da tsada. A cikin Shirin, Hukuma na Jihar Legas za ta:-

  • Bada gidaje masu kyau kuma da araha na iri-iri masu girmomi daban-daban, kuma za a iya samu a yawancin wurare cikin Jihar Legas.
  • Ba wa masu zaman a Jihar Legas wanda Masu Siya-da Farko kenan daman samun aron kudin gida domin su siya gidajen nan.

  Wannan Shiri an yi dalilin ba wa masu zama a garin Legas yancin samu mallakin gida na kansu, a kuma hana mutanen da suna da gidaje da yawa daga siyawa saboda kar su batta shiri din wanda an kera domin bada gidaje masu  araha.

 • WANENE MAI SIYA-NA FARKO?

  +

  Masu zaman a Jihar Legas wanda suna zuwa kasuwancin gida da farko, sune ana kira Masu Siya-Da Farko. Masu Siya Da Farko ba su da kowane gida a da; kuma ba sua cikin duk wanda Jihar Legas ta ba wa kasa domin yin gini  a lokacin baya.  Masu Siya Da Farko ba su da mallakin kowane arzikin kasa ko gida (ko rabi ko cikakke) cikin Jihar Legas kuma za su yi rantsi wato Takardar Tabbatawa na Majalisar Shari'awanda zai tabbatar da cewa su Masu Siya Da Farko ne da gaske.

 • TA YAYA NE SHIRIN NAN YAKE AIKI?

  +

  Idan an gama ginin, za a ba wa Taro Mai Kula da Siyawa Cikin Aro wato (“su LMB”) domin su raba ma wanda ya kamata. 

  Ita LMB din za ta tabbatar da ingancin wanda sun yi rajista domin wannan shiri, saboda su shiga cikin wani Wasan Ci, wanda za a ta yi kullum, a wannan lokacin kuma Kamfanin Sa Kudi cikin Gini Ltd wato (LBIC) za ta gudanar da kudin Siyawa Cikin Aron ma wanda sun ci nassara saboda su siya gida. Danna akan wannan mahadi wato Menene Ya Kamata In Sani?akan wurin gizon HOMS na Legas wato(www.lagoshoms.gov.ng).  domin samun karin bayyani akan batun  yadda shirin yake aiki.

 • WANENE YA KAMATA YA YI RAJISTA?

  +

  Duk masu zama a Jihar Legas wanda sun iso shekaru ashirin da daya, wanda kuma sunCika Bukatun da Ana So  na Shiri din nan, su ne za su iya yin rajista.

 • BAI DADDE BA DA NA DAWO DAGA KASAR WAJE INDA NIKE ZAMA CIKIN SHEKARU UKU MASU WUCEWA. KO NI MA NA CIKA BUKATUN YIN RAJISTA DOMIN SHIRIN?

  +

  Kowane mutum da ya  Cika Bukatun da Ana So  yanada daman yin rajista. Kodayake, Shirin tana da bukatu cewa wanda suna zama a Jihar legas kawai ne ya kamata su shiga cikin Masu Yin Rajista, su kuma kasance masu biyan haraji tare da nunawa takardan shaida na haraji da sun biya shekaru 5 (biyar) masu wucewa kafin su yi rajista.

 • KO YAN MAKARANTA MA ZA SU IYA YIN RAJISTA?

  +

  Dokan wannan shiri yana cewa duk wanda za su yi rajista su Cika Bukatun da Ana So  ,wannan yana hade da bayarwa shaida na biyan haraji na shekaru biyar masu wucewa da kuma shaida cewa suna samu kudi daga wanni sana’a wanda zai sa su iya biya kudin wata-wata na shirin. Idan yan makaranta suna da wannan, to sun cika bukatun kenan.

 • 7. AKWAI IYAKAN SHEKARAN MUTUM DA AKA SO WANDA ZAI HANNA NI DAGA YIN RAJISTA ZUWA CIKIN SHIRIN SIYA CIKIN ARO NA HOMS DIN LEGAS?

  +

  Iyakan shekaru da ana bukata shine shekaru ashirin da daya, in ya yayi kasa da wannan to mutumin bai cika bukatan HOMS na Legas ba kenan. Amma ba a sa shekaru mafi sama ba. Tsayin cika bukatu naka zai danganta kan yadda kake biya kudin wata-wata naka wanda shirin zai bukata.

 • ZAN IYA SAMU ABOKIN-RAJISTA, WATO WANDA ZA MU YI ARON TARE DA SHI?

  +

  E’e, amma dai za a so ku biyu a matsayin kanku ku cika bukatun da an kera cikin Shirin HOMS na Legas kuma za a ba ku batun Hadadden Mallaki na gidan in ku ci nassara.

 • A INA NE ZAN SAMU KARIN BAYANI A KAN BATUN GIDAJEN DA SUKE AKWAI?

  +

  Ziyarci  http://www.lagoshomes.gov.ng/homes  domin samun girma, iri da wurin da gidaje suna akwai.

 • INA SON SHIGA CIKIN SHIRIN HOMS NA LEGAS. YA NE MATAKIN SHIGOWA?

  +

  Danna kan Mahadi na Mataki Biyar Masu Sauki domin samun bayani a game da mataki biyar masu kara saukin samu mallakin gidanka.

 • NAWA NE KUDIN SHIRYE-SHIRYE DOMIN SHIGO SHIRIN, KUMA ZA A SAKE BIYA NI KUDIN IDAN BAN CI NASSARA A WASAN CI DIN NAN?

  +

  Kudin shirye-shirye domin shigo shirin N10,000.00 ne wato (naira Dubu Goma). Kudin gudanar da shirye-shirye din nan ne kuma ba za a sake-biya kowane mutum ba, kuma dole ne ka biya kudin kafin ka aika takardan rajista da ka yi.

 • ANA BUKATA IN AIKA TAKARDAN RAJISTA DIN NAN TARE DA WANI ABU KUMA?

  +

  Za ka iya samu jerin daftarai da ya kamata ka aika tare da takardan rajista din ka  akan takardan rajista din da kuma kan wurin gizo. Danna kan Mahadi nan Jerin bincike na Daftarai domin Aika Takardan Rajista Naka. 

 • MAI ZAI FARU BAYAN WASAN CI?

  +

  Idan ka ci nassara a Wasan Ci, su LBIC za su fara gudanar da Shirye-Shiryen Siya Cikin Aro Naka ta hanyar aika maka wani Wasikar Taya, wanda za ka nuna cewa ka yarda da dokokin shirin yadda LBIC sun kera, had da yi biyawan talatin bisa dari na cikin lokacin da an ce ka biya a Taya din  nan. A lokacin kuma za yi san hannu a kan Yarjejeniyar Siyarwa da Takardan Shaida Mulkin Gida na Siya Cikin Aro sai a ba ka makullin gidan.

 • ME ZAI FARU IN BAN YI NASSARA A WASAN CI BA?

  +

  Za ka iya sake-yin rajista da yawa yadda kake so amma za a bukata ka biya kudin gudanar da shirye-shirye a kowane lokaci da ka yi rajista. Kodayake, idan kana sake-yin rajista cikin watanni uku da ka yi wancan rajista na farko kuma bayananka ba su canza ba, ba za ka bukata sabon takardan rajista ba. Kawai za a bukata ka kawo  Takardar Tabbatawa da Yin Rajista na Majalisar Shari'a .

 • TA YAYA NE ZAN SAMU SANIN CEWA NA CIKA BUKATA DOMIN SHIGO SHIRIN SIYA CIKIN ARO A KARKASHIN HOMS NA LEGAS?

  +

  Wannan mai sauki ne. Danna akan Tab na Kayayaki  akan wurin gizo na HOMS din Legas, wanda zai giya ma ka duk abubuwa da kana son sani. Za ka iya yi amfani da Kwakwaletan Siya Cikin Arodomin ka lissafa kudin da ana bukata ka biya a kowane wata.

 • MENENE RIBAN DA ZA A BIYA AKAN SHIRIN SIYA CIKIN ARO NA HOMS DIN LEGAS?

  +

  Riban da an rege daban-daban ne. Danna nan domin samun kiman riba na kwanan nan  

 • MENENE LOKACI MAFI KASA DA ZA A IYA BIYA KUDIN SIYA CIKIN ARO WANNAN.

  +

  Lokaci mafi kasa da za a ba ka domin biya kudin siya cikin aro a shirin HOMS din Legas shine shekaru 10 (Shekaru Goma)

 • YA NE ZAN SANI KUDIN DA YA KAMATA IN BIYA NA SHIRIN SIYA CIKIN ARO?

  +

  Domin yin lissafin jimlar kudin da ya kamata ka biya na siya cikin aro, dannan  Kwakwaletan Siya Cikin Aro.  Wannan zai sa ga gan yadda siya cikin aro nan yana aiki. Zai nuna maka nawa cikin kudin da za ka biya wata-wata yana nufa riba, da kuma wanda yana nufi kudin gidan [wato ainihin kudin da ka ara]

 • WHAT IS MY EQUITY CONTRIBUTION?/MENENE BIYAWAN EKWITY NAWA?

  +

  Masu yin rajista wanda sun ci nassara a Wasan Ci za su biya wani kudin da zai yi daidai da darajan gidan da suna son siya har zuwa talatin bisa dari wato 30%. To wannan ne ana kira Biyawan Ekwity.

 • WANE KUDI KUMA ZA A KARA MUN IN BIYA IDAN NA YI WANNAN SHIRIN SIYA CIKIN ARO?

  +

  /Kudin kammala da kasuwancin gidan kawai ne za ka biya, had da kudin buga hatimi da kudin san hannu. Kodayake, idan ka shiga gidanka, za ka ci gaba da biyan kudin kulawa da gida yadda ya kamata  kamar kudin inshuara, kudin kula da kayan gida, kudin yin amfani da kasa, da sauransu. Cikin duk misalan nan, kudin da za ka biya zai danganta kan darajan gidanka.

 • DOLE NE IN BUDA ASUSU DA LBIC?

  +

  Eh ya kamata ka bude wani asusu da LBIC inda za a rika biya kudin shirin siya cikin aro dinka. Dole ne kuma ka sa kudi cikin asusun a kowane wata domin biya kudin siya cikin aro.

 • KO ZA A BAR IN BADA CEK NA BANKI WANDA AN MATSA LOKACIN KARBA KUDINSA ZUWA WATA RANA A GABA SABODA BIYAWA KUDIN SIYA CIKIN ARO NAWA?

  +

  Eh, za ka iya bada cek na banki wanda an matsa lokacin karba kudinsa domin ka biya cikin asusun LBIC a kuma yi amfani da shi a biya kudin wata-wata na ka.

 • KO ZA A IYA CIRE KUDIN SIYA CIKIN ARO NA DAGA CIKIN WANI KUDIN NA A BANKI DABAN DA NA SHIRIN?

  +

  A'a, amma za ka iya saita shirin da zai sa a rika cire kudi daga asusun na banki daban a sa cikin asusun LBIC naka.

 • TA YA NE ZAN DUBA KUDIN SIYA CIKIN ARO NA WANDA YA REGE.

  +

  Za ka iya duba kudin da ya rege cikin shirin siya cikin aro ta hanyan tuntuba ofishin Masu Kula da Abokanan Ciniki a LBIC.

 • KO ZA A BAR IN BIYA FIYE DA KUDIN BIYAWA EKWITI WATO TALATIN BISA DARI IDAN INA DA KUDIN A HANNU?

  +

  A'a ba za a bar ka biya haka ba. Kawai za a so ka yi biyawan ekwiti har zuwa talatin bisa dari kuma kudin da za ka biya a wata-wata dole ne kar ya wuce kiman talatin bisa dari wato 30%.

 • MENENE YANA FARUWA A YAYINDA ANA GUDANAR DA TAKARDAN RAJISTA NA?

  +

  Idan ka cika Wasan Ci, za a aika shi zuwa LBIC domin shiryawa. Danna akan Mahadin Gudanarwa da Shirye-shiryen Siya Cikin Aro domin ka samu karin bayani akan batu abubuwa da ana yi a mataki-zuwa-mataki- a lokacin shiryawan takardan rajistan ka na shirin siya cikin aro

 • MAI TSAWON LOKACI DA SHIRYE-SHIRYEN TAKARDAN RAJISTA NA SHIRIN SIYA CIKIN ARO NAWA ZAI DAUKA?

  +

  Wannan zai danganta kan lokacin da za ka dauka a cikawan bukatun da LBIC take so, amma ba zai wuce kwanaki talatin ba.

 • ZA A BAR IN RIKA DUBA MATSAYIN SHIRYAWA NA TAKARDAN RAJISTA NAWA NA SIYA CIKIN ARO?

  +

  Eh za ka iya duba, ta hanyan danna kan Mahadi na Bi Sawun Takardan Rajista na akan wurin gizo na HOMS din Legas.

 • KO ZA A BAR IN CIKA BIYAWA KUDIN SIYA CIKIN ARO NA KAFIN

  +

  A'a. Lokacin biya mafi kasa na shirin siya cikin aro wanda na Shirin HOMS din Legas shine shekaru 10 (shekaru goma). 

 • 31. ZA A BAR IN KARA KUDIN DA ZAN BIYA A WATA-WATA?

  +

  Eh, za a yarda idan wannan ba zai rege lokacin biya mafi kasa wanda an sa shekaru goma ba.

 • ME ZAI FARU IN NA RASA BIYAWA KO IN NA MAKARA A YIN BIYA NA?

  +

  Idan ka rasa biya watanni uku masu bin juna, za a zo a yi Rufe-Kafin a gidan da an siyar ma ka. In ka makara a biya, za ka biya ladan kudin da zai yi daidai da ashirin bisa dari. Ana bada shawara ka tuntuba LBIC maza-maza in ka gani cewa za ka samu matsalan biyawa.

 • MENENE BATUN DAFTARI NA GIDAN KUMA YA ZAN SAMU SHI IDAN NA CI NASSARA?

  +

  Za a bada daftarin batu a zaman Rabin-Bayarwa daga Gwamnatin Jihar Legas a shekaru casa'in da tara da cirewan kwana daya.Za a shirya maka wannan domin ka sa hannu yayinda ka cika shirye-shiren siya cikin aro din nan, amma Masu bada shirin siya cikin aron za su rike takarda har sai ka gama duk biyawanka na gidan, an kuma rufe biyawan aron.

 • ZAN BUKATA INSHUWARA?

  +

  Eh, za a bukata ka yi Inshuara Arziki na dole domin ya ka samu kariya daga wuta da sauran matsalolin hanzari. Wannan ne daya daga cikin dokan da LBIC ta jera ma shirin. Wan kuma shine Inshuara na Kare Siya Cikin Aro, ba a ce dole ne ka yi wannan ba amma ana shawarta ka yi shi saboda yana kare ka daga matsalolin mutuwa da nakassaanci.

 • ZAN IYA BADA GIDA NA HAYA?

  +

  A'a. Shirin HOMS din Legas shiri ne na MAI MALLAKI-MAI ZAMA. Wannan yana nufi cewa dole ne ka zama cikin gidan da ka siya. Ba za a yarda ka bada gidan da ka siya haya ba, kuma za a rika yi binciken gidaje kullum saboda masu gidan su bi dokan.

 • BAN GAMA BIYA KUDIN SIYA CIKIN ARO NA BA AMMA INA SO IN SAYAR DA GIDA NA.

  +

  Sayarwa da gidanka a lokacin da ba ka gama biya kudin siya cikin aro naka yana nufi cewa kana so ka cika biyawanka din nan kuma za ka iya yi wannan kawai daga wurin LBIC. Domin cika biyawanka dole ne ka tuntube LMB, wanda za su tamaika ka yadda ya kamata.

 • KO INA BUKAATA LAUYA WATO WAKILI?

  +

  Eh, ana shawarta sosai cewa ka samu shawara daga wurin lauya domin ya nuna maka yadda za ka bi bukatun sharia.

 • WANENE ZAI KULA DA GYARAWAN GIDA NA BAYA NA SIYA?

  +

  Akwai wadansu kamfanoni masu kula da Gyare-gyaren Kayen Gida wanda LMB za su bada, wanda kuma aikin su zai kumsa gyarawan kayan waje na gida da hidimomin wurare da ya kamata. Masu mallakin gidan ne za su biya kudin kamfanonin nan ta hanyan biya kudin hidimomi na kulluma wanda za a bada. Kodayake, za a bukata mai mallakin gidan ya kula da gyare-gyaren kaya a cikin gida.

 • NI WAKILIN KASUWANCIN GIDAJE NE, KUMA INA SO IN SIYA GIDAJE MA ABOKANAN CINIKI NA CIKIN WANNAN SHIRI.

  +

  Saboda wannan shiri na masu mallakin gida ne kawai, muna yaba da cewa ka giya ma abokanen cinikinka su yi rajista da kansu domin samu gidaje da suka so wato ba a yarda da wakilan kasuwanci a wannan shiri.

***APPLICANTS ARE STRONGLY ADVISED TO SEEK THE ADVICE OF A LAWYER TO ASSIST THEM THROUGH THE MORTGAGE APPLICATION PROCESS


Back to TopBack to Top